IQNA

Mutane 463 ne za su shiga gasar kur'ani mai tsarki a watan Ramadan a kasar UAE

19:31 - April 01, 2022
Lambar Labari: 3487112
A ranar Litinin 6 ga watan Afrilu ne za a fara gasar nakasassu karo na goma a watan Ramadan, tare da halartar makaranta 463 da za a dauki tsawon makonni biyu ana yi.

A cewar shafin yada labarai na "alkhaleej.ae", mahalarta 463 daga cibiyoyi da kasashe 57 ne za su shiga cikin gasar a wannan lokaci, wanda za a shafe makonni biyu ana gudanarwa a hedkwatar hukumar kula da wutar lantarki ta Dubai.

Ana gudanar da wannan gasa a fannoni daban-daban na haddar Alkur'ani gaba daya, da haddar kashi  20, da haddar rabin kur'ani, da haddar kashi 10, da haddar kashi 7, da haddar kashi 5, da haddar sassa uku, da haddar bangare biyu, da haddar bangare daya. da haddar gajerun surori na Alkur'ani.

Mamba a kwamitin gudanarwa na gasar Ra'isa Al;-falasi ya ce: “Wannan gasa na da nufin karfafa gwiwar masu hazaka wajen haddace lafuzzan wahayi da yin tunani a kan ma’anonin kur’ani, da kuma gano sabbin hazikai na kur’ani a tsakanin wannan bangare  kungiya ta Al’umma.

Ya kara da cewa: "Masu nakasa da ba za su iya halartar hedkwatar din Dubai Towers don halartar wadannan gasa ba, za su iya shiga wadannan gasa ta yanar gizo."

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045961

captcha