A kowace shekara a wanann lokaci cibiyar ta kan gudanar da wani majalisi na karatun kur’ani mai tsarki, inda makaranta kur’ani da mahardata sukan halarta daga kasashe daban-daban.
A wanann shekarar sakamon matsalolin da ake fuskanta ta fuskar kiwon lafiya, cibiyar tana gudanar da taron ne ta hanyar yanar gizo, inda ta saka tilawar daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani dan kasar Iran Karim Mansuri.
Wannan makaranci ya kasance yana halartar gasar kur’ania cikin gida tun fiye da shekaru talatin da suka gabata, ya kuma fara wakiltar kasar Iran a tarukan gasar kur’ani na duniya a shekara ta 1991, inda ya zo a mataki na daya alokuta daban-daban.