IQNA

Wani Jami’in Gwamnatin Sudan Ya Yi Batunci Ga Addini

16:16 - May 08, 2020
Lambar Labari: 3484775
Tehran (IQNA) daraktan cibiyar tsara manhajar karatu ta kasa a Sudan ya bukaci da a cire kur’ani daga cikin manhajar karatu a makarantun share fagen shiga firamare.

Shafin yada labarai na almustaqbal ya bayar da rahoton cewa, Umar Ahmad Alqarai Babban daraktan cibiyar tsare-tsaren manhajar karatu da kuma kula da ayyukan madaba’antu a Sudan, ya mika bukatarsa ta neman a cire kur’ani daga cikin manhajar karatu a makarantun share fagen shiga firamare a fadin kasar Sudan, bisa hujjar cewa koyar da wasu abubuwa da ke cikin kur’ani ga kananan yara yana tattare da hadari.

Wannan lamari ya fuskanci kakkausan martani daga ko’ina  a cikin fadin kasar ta Sudan, tare da bayyana wannan furuci da cewa yana a matsayin batunci ga kur’ani mai tsarki da ma addinin muslunci baki daya.

A kan haka jama’a suna ci gaba da yin kira ga sabbin mahukuntan kasar ta Sudan da su gaggauta daukar matakin tsige wannan jami’i daga kan mukaminsa, sannan kuma a hukunta shi a kan kalaman da ya furta dangane da kur’ani mai tsarki.

 

3897207

 

 

 

 

captcha