Kamfanin dillancin labaran IQNA, cibiyar darul kur’an na da shafukan yada zumunta da take saka abubuwa ad suka danganci addini.
Wannan cibiya ta saka karatun kur’ani na Amir Hussain Bagheri wani matashi dan kasar Iran da yake karatun kur’ani da irin salon Karin harshe irin na marigayi Abdulbasit Abdulsamad.
Amir Hussain Bagheri ya yi karatun nasa ne a gasar kur’ani mai tsarki ta Isra da aka gudanar wadda tashar kur’ani ta hukumar radiyo da talabijin ta Iran ta dauki nauyin gudanarwa.
https://iqna.ir/fa/news/3876127