Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wannan makon ne ma'aikatan cibiyar agaji ta musulmin kasar Afirka ta kudu Gift of the Givers ta isa kasar Haiti domin kai taimako ga al'ummar kasar .
Rahoton ya ce wannan kugiya wadda musulmin kasar Afirka ta kudu masu hannu da shuni suka kafa, tana gudanar da ayyuka na jin kai a kasashen duniya da dama.
Daga cikin irin ayyukan da kungiyar ke gudanarwa har da gina makarantu a yankuna na marasa galihu, da kuam samar da madatsun ruwa, da gina kwalbati.
Baya ga haka kuam a bangaren ayyukan kiwon lafiya kungiyar tana guanar da ayyuka na samar da magunguna ga mabukata, da kuma gina dakunan shan magani.
Yanzu haka dai a kasar Haiti kungiyar tana gudanar da ayyuka na tallafawa jama'a a bangarori na kiwon lafiya da ilimi, da kuma samar da ruwan sha a wasu yankunan da suke fuskantar matsala a wannan bangare.