IQNA

Gwamnatin Falastinu Ta Bude Rediyo Da Harsunan Ingilishi Da Hibru

16:17 - November 07, 2021
Lambar Labari: 3486522
Tehran (IQNA) gwamnatin Falastinawa ta bude rediyo da harsunan Ingilishi da kuma Hibru.

An kaddamar da gidan radiyon farko na Falasdinawa a cikin harshen Ingilishi da yahudanci da nufin ba da haske kan hakikanin abubuwan da ke faruwa a yankunan Palasdinawa sakamakon hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahyuniya suke yi, da kuma kokarin mayar da birnin Quds na yahudawa zalla.

Rima Mustafa wata mai watsa labarai a gidan rediyon Quds 24 a harshen Hebrew ta ce, gidan rediyon ya fara aiki ne watanni uku da suka gabata kuma yana ba da labarin muhimman abubuwan da suka faru a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, da kuma bayar da labarai na gaskiya a tashar.

Ta ce ta yi imanin cewa mutanen da ke zaune a yankunan da aka mamaye suna buƙatar ƙarin tashoshi domin smun bayanai, don haka suna maraba da bude wannan rediyo.

Abu Asab, editan gidan rediyon ya ce; "Dole ne duniya ta fahimci halin da ake ciki da kuma gaskiyar abin da ke faruwa, a kan haka za mu bayar da muhimmanci wajen yada labarai da turancin ingilishi da kuma Hebrew.

 

4010925

 

captcha