IQNA

Jordan Za Ta Samar Da Wani Shiri Na Yawon Bude Ido Ga ‘Yan Najeriya

14:47 - November 06, 2021
Lambar Labari: 3486518
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Jordan na da wani gagarumin shiri na jan hankalin ‘yan Najeriya masu yawon bude ido.

Kasar Jordan na kokarin jawo hankalin masu yawon bude ido ne  a fannonin yawon bude ido na addini, kiwon lafiya da kuma nishadi.

A baya-bayan nan dai Masarautar kasar Jordan ta zama wurin hutu ga ‘yan Najeriya ta fuskar harkokin yawon bude ido.

Kasar dai na da wuraren da musulmi da kiristoci ke zuwa ziyara, kamar yadda kuma akwai daya daga cikin abubuwan al'ajabi bakwai na duniya da ke kasar Jordan, wato Petra.

A kwanakin baya ne kasar Jordan ta kaddamar da wannan shiri na musamman na gabatar da masu yawon bude ido daga Najeriya tare da hadin gwiwar wani kamfanin yawon bude ido na Najeriya dake da ofisoshi Legas da Kano.

Tawagar wakilai daga hukumar kula da yawon bude ido ta kasar Jordan da suka hada da kwararru a fannin yawon bude ido, likitoci da kuma masu ba da shawara kan harkokin addinin musulunci, na daga cikin masu halartar taron kaddamar da wannan shiri.

Shugaban hukumar yawon bude ido ta Jordan Abdul Razzaq Arabiat ya ce "Najeriya wata sabuwar fuska ce ta kasuwar yawon bude ido ta Jordan.

" Shirin na da nufin kara wayar da kan ‘yan Najeriya game da kasar Jordan a matsayin wurin yawon bude ido da suka hada da bangarorin addinin Musulunci, Kiristanci, Likitanci, Jiyya, Ilimi da Nishadi.

"Annobar Corona ta yi mummunan tasiri a harkokin yawon bude ido a duniya," in ji Elizabeth Egbola, daraktar Cibiyar Kula da Balaguro ta Najeriya.

 

4010975

 

captcha