IQNA

Makarantu Da Cibiyoyin Kur’ani Dubu 20 Ne Suke Gudanar Da Ayyukansu A Aljeriya

22:26 - January 05, 2021
Lambar Labari: 3485527
Tehran (IQNA) an bude makarantu da cibiyoyin kur’ani mai tsarki guda dubu 20 a cikin kasar Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran sabaq press ya bayar da rahoton cewa, minista mai kula da harkokin addini a kasar Aljeriya Yusuf Bilmukhtar ya bayyaa cewa, a halin yanzu makarantu da cibiyoyin kur’ani mai tsarki guda dubu 20 da 500 a cikin kasar Aljeriya.

Y ace a cikin birnin Aljiers fadar mulkin kasar akwai dalibai a makarantun kur’ani da yawansu ya kai dubu 800 da 500 da suke karatu.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa a cikin babban birnin akwai makarantu 58 da kuma cibiyoyi 1010 da suke gudanar da ayyuka a bangaren kur’ani mai tsarki.

Ya kara da cewa, ci gaba da ake samu tafuskacin ayyukan kur’ani a makarantu da cibiyoyin addini a kasar Aljeriya da kuam karuwar yawan daliban da suke koyon ilmomin kur’ani na nuni da yadda al’ummar kasar suka himmatu da lamarin kur’ani.

 

3945732

 

 

 

captcha