IQNA

Biden Zai Janye Dokar Trump Wadda Ta Hana Musulmi Daga Wasu Kasashe Shiga Amurka

0:54 - November 10, 2020
Lambar Labari: 3485351
Tehran (IQNA) Joe Biden zai kawo karshen dokar Donald Trump ta hana izinin shiga ga wasu daga cikin kasashen musulmi.

Dan takarar shugabancin Amurka da ya lashe zabe Joe Biden, na da nufin kawo karshen dokar da Donald Trump ya kafa, ta hana izinin shiga ga wasu daga cikin kasashen musulmi a cikin Amurka.

Jaridar Washington Post ta bayar da rahoton cewa, bisa ga bayanan da wasu makusantan Joe Biden suke yi, na tabbatar da cewa Biden na da nufin kawo karshen dokar nuna wariya ga wasu daga cikin kasashen musulmi da Donald Trump ya kafa.

Tun a cikin shekara ta 2017 ne dai Donald Trump ya kafa dokar da ta haram wa wasu kasashen musulmi izinin shiga cikin kasar Amurka, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen kasar ta Amurka.

A nata bangaren babbar kungiyar musulmin kasar ta Amurka ta fitar da wani bayani da ke cewa, kungiyar tana kiran Joe Biden da mayar da hankali wajen aiwatar da alkawullan da ya dauka, musamman na kare hakkokin musulmia kasar Amurka, tare kawo karshen nuna musu wariya a kasar.

A cikin shekaru hudu da Donald Trump ya yi yana mulkin Amurka, musulmi sun fuskanci matsaloli masu tarin yawa akasar, domin kuwa a lokacin mulkinsa ne kyamar musulmi ta kara tsananta a kasar Amurka, sakamakon irin kalaman da yake na tozarta musulmi da kuma yin batunci a kansu.

 

3934079

 

 

captcha