Karatun kur’ani na Sheikh Abdulbasit Abdulsamad inda ya karanta aya ta 6 zuwa 8 a Surat Infitar.
Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci (6)
Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka (7)
A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta (8)