IQNA

An Gayyaci Kasashe Fiye 100 Domin Halartar Gasar Kur’ani A Masar

21:47 - November 04, 2019
Lambar Labari: 3484221
Bangaren kasa da kasa, an gayyaci kasashe fiye da 100 domin halaratr gasar karatu da harder kur’ani a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna , shafin yada labarai na yaum sabi ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta bayar da sanarwar cewa; ta aike da goron gayyata zuwa ga kasashe fiye da 100 domin halartar gasar kur’ani ta kasa da kasa karo na 27 da za a gudanar a kasar.

Baya ga kasashe 40 na Afrika, an aike da goron gayyata zuwa ga kasashe da daman a larabawa, Rasha, Balkan, Serbia, Bosnia, Bolgaria, Girka da kuma wasu daga cikin kasashen nahiyar turai da kuma latin Amurka.

Bayanin ma’aikatar kula da harkokin addinan ta kasar Masar ya ce, a halin yanzu ana tattaunawa da kasashen da musulmi su ne ‘yan tsiraru, domin samun halartar gasar.

3854676

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha