IQNA

An Girmama Wadanda Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur'ani ta Karbala

23:47 - April 04, 2018
Lambar Labari: 3482539
Bangaren kasa da kasa, an girmama wadanda suka nuna kwazoa gasar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin karbala.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar darul kur'an cewa, a jiya an girmama wadanda suka nuna kwazoa  gasar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin karbala na kasar Iraki.

Jami'ar muslunci ta Karbala ce ta dauke nasuyin shirya wannan gasa, wadda ta kunshi mata zalla, kuma an bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, yayin da kuma aka bayar da wasu kt\yutuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

Dalibai 70 daga jami'oi daban-daban da suka hada da Kufa, Babul Basara da Karbala da sauransu suka halarci, wadda aka gudanar a bangarori na hardar kur'ani.

Abin tuni a nan shine jami'ar musulunci ta Karbala dai tana karkashin hubbaren Imam Hussain amincin Allah ya tabbata a gare shi ne.

3703061

 

captcha