Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka yi a zirin Gaza da aka kwashe tsawon kwanaki 7 ana yi ta kawo karshe da karfe 7 na safe agogon kasar a yau Juma’a.
Ofishin yada labarai na jihar Gaza ya sanar da cewa, jiragen saman mamaya sun kai hare-hare a kudancin zirin Gaza. Kazalika, majiyoyin cikin gida sun sanar da cewa 'yan mamaya sun kai hari a yankunan Sheikh Rezwan da kuma arewacin birnin Gaza.
A hukumance sojojin yahudawan sahyoniya sun sanar da sake komawa fada da kungiyar Hamas a zirin Gaza. Avikhay Adrei kakakin sojojin gwamnatin sahyoniyawan ya yi ikirarin cewa: Hamas ta karya yarjejeniyar tare da harba harsasai kan Isra'ila.
Ya ce: Sojojin Isra'ila sun sanar da sake kunna wuta a arangamar da suka yi da Hamas.
Adrei ya kara da cewa: Bibiyan kunna siren gargadi a Kibbutz Havlit ya nuna cewa an harba rokoki da dama daga zirin Gaza zuwa Isra'ila, wadanda aka kama.