Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq al-Arabiya cewa, karuwar dabi’ar addinin muslunci a shekarun baya-bayan nan ya kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da suka nuna yadda addini ya kasance a Amurka.
Da dama dai sun gabatar da addinin Musulunci a matsayin addini na farko wajen karuwar mabiya a Amurka, kuma da dama sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 2040, Musulunci zai zarce addinin Yahudanci kuma ya zama addini na biyu a Amurka.
A shekarun baya-bayan nan dai an zargi Musulman Amurka da kara nuna kyama da kuma tuhume-tuhume daban-daban da suka hada da goyon bayan ta'addanci, sannan kuma sun sha kokawa kan yadda 'yan sanda da hukumomin tsaro ke nuna musu wariya musamman bayan abubuwan da suka faru a ranar 11 ga watan Satumba.
Bayan farmakin guguwar Al-Aqsa da kuma ayyana goyon bayan musulmi ga al'ummar Palastinu, wadannan zarge-zarge sun sake tasowa.