Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin Reuters ya nakalto daga shafin A’amaq na kungiyoyin ‘yan ta’adda masu akidar takfir cewa, a cikin wannan mako sun kashe tare da jikkata sojojin Najeriya 40 a cikin Jahar Borno.
Babu wata majiya da ta tababtar da wanann rahoto, amma wasu mazauna wasu kauyuka a cikin jihar Bornon sun tababtar da cewa a ranakun Litinin da Talata sojojin Najeriya sun yi bata kashi da ‘yan ta’adda.
Baya ga haka kuma ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai wasu hare-hare a cikin wannan mako a kan fararen hula a jihar ta Borno, inda suka kashe mutane 65 a lokacin gudanar da wata jana’iza.