IQNA

Mayakan Boko Haram Sun kashe Sojojin Najeriya 13

23:58 - December 26, 2018
Lambar Labari: 3483255
Bangaren kasa da kasa, a wani harin kwantan bauana da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wa sojojin najeriya sun kashe13 daga cikin sojojin a cikin jahar Yobe.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, bisa wani bayani da ya fito daga rundunar sojin Najeriya, mayakan Boko Haram sun dana wa sojojin wani tarkoa  kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, inda suka kashe sojoji 13 da dan sanda guda.

Wannan harin na zuwa ne bayan wani makamancinsa da mayakan an Boko Haram suka kai wa sojojin a cikin jahar Yobe a cikin wanann mako, wanda wanda shi ma aka barin wuta tsakanin sojojin da kuma mayakan an Boko haram, duk kuwa da cewa sosjojin sun ce sun kasha wasu daga cikin maharani, yayin da soja guda ya rasa ransa.

To sai dai wasu majiyoyin na daban da suka hada da wasu mutanen yanin da abin ya faru da ma wasu jami'an tsaro, sun sheda wa kamfanin dilalncin labaran AFP cewa sojoji 18 ne mayakan an Boko Haram suka kashe a harin na kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

3775900

 

 

 

 

captcha