IQNA

Alkawarin Bayar Da Taimakon Kudade Ga Kasashen Da Boko Haram Ta Addaba

23:22 - September 04, 2018
Lambar Labari: 3482953
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Jamus ta yi alkwarin bayar da wasu makudaden kudade a matsayin tallafi ga kasashen da Boko Haram ta addaba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, a zaman da aka gudanara  jiya a birnin Berlin na kasar Jamus da nufin samo taimako domin tallafa wa yankunan da rikicin Boko Haram ya yi illa, gwamnatin Jamus ta ce za ta vayar da Yuro biliyan 2.7 ga kasashen yankin tabkin Chadi, wato Nijar, Najeriya, Kamaru da kuma Chadi.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus ta ce manufar hakan ita ce tallafa wa wadannan kasashe hudu domin shawo akn matsalar da ake fuskanta a yankunan da Boko Hara ta yi wa yankan kauna.

A kwanakin bayan ne wasu kungiyoyin farar hula na kasa da suka fitar da rahotanni da ke cewa, akalla mutane miliyan 12 ne suke bukatar taimakon gaggawa a yankunan da ke makwabtaka da tafkin Chadi, sakamkon matsalolin da rikicin Boko Haram ya haddasa musu.

A jiya ne aka fara zaman taron an Berlin, tare da halartar wakilai daga kasashne hudu na yankin tabikin Chadi da kuma jami'an gwamnatin Jamus, wanda za a kammala yau Talata.

3743928

 

 

 

captcha