Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, China ba ta gamsu da rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar ba, wanda yake dora alhakin kisan musulmin Myanmar a kan sojojin gwamnatin kasar.
A lokain da take asa tambayoyin manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin China Huwa Chinying a yau Talata, a lokacin da aka tambaye ta kan rahoton kwamitin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya kan kisan kiyashin musulmin Rohingya, wanda aka zargi sojojin gwamnatin kasar da aikatawa, ta bayyana cewa wannan zargi ba shi ne mafita ba.
Kasar China wadda take bin addinin buda, tana da kyakkyawar alaka da gwamnatin kasar Myanmar wadda ita ma take bin addinin na buda.
Ga dukkanin alamu China za ta hana daukar duk wani mataki na ladabtarwa a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan gwamnatin Myanmar an kisan musulmin Rohingya.