IQNA

Sakon Wani Yaro Bafalastine Zuwa Ga Majalisar Dinkin Duniya

23:34 - June 05, 2018
1
Lambar Labari: 3482729
Bangaren kasa da kasa, an yada wani sako daga wani yaro bafalastine zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kafofin yada labarai na yanar gizo sun watsa wani sako na wani yaro bafalastine zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya dangane da halin da suke ciki.

A cikin sakon, yaron ya ce wai ian majalisar dinkin duniya da kasashen larabawa suke ne?

Shin me yasa suka zura ido suna kallon Isra’ila  akullum rana tana yi wa palastinawa kisan kiyashi ba tare da sun ce uffan ba balantana su taka mata burki?

Ya ci gaba da cewa yana yin kira ga majalisar dinkin duniya da ma sauran al’ummomin duniya masu sauran lamiri da jin ka a cikin rayukansu, da su tuna da halin da yaran Palastinawa suke ciki.

Ya ce yaran palastinawa kamar sauran yaran kasashen duniya, suna son su rayu ba wai su mutu ba, a kan haka su taimaka su kame hannun Ira’ila tare da hana kisan yaran palastinawa da saka su gidajen kaso.

3720540

 

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Saidu Lawal Tukur Mairua
0
0
Ina Farincikin Da Wannan Kafa Yaune Nafara Cinkaro Da Ita Allah Yaijagoranci
captcha