IQNA

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Kiyashin Da Isra’ila Ke Ya Wa Palastinawa

23:48 - April 01, 2018
Lambar Labari: 3482530
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da kisan kiyashin Isra’ila ta yi kan Palastinawa a Gaza.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, Bahram Qasemi kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; gwamnatin kasar Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da kisan kiyashin Isra’ila ta yi kan Palastinawa a Gaza a ranar Juma’a da ta gabata a ranar tunawa da cikar shekaru arbain da biyu da kwace wa Palastinawa yankuna a Gaza.

A cikin bayanin nasa Qasemi ya bayyana cewa, ko shakka babu abin da Isra’ila ta yi kuma take ci gaba da kan al’ummar Palastinu lamari ne da ke kara fito da hakikanin wace ce isra’ila, da kuma irin mummunan kudirin da suke da shi a kan al’ummar musulmi.

Ya kara da cewa, abin ban mamaki shi ne yadda wasu daga cikin larabawa na yankin gabas ta tsakiya suke ta hankoron ganin sun kulla alaka da Isra’ila, daga ciki har har da masu tinkaho da sunan musulunci,a  daidai lokacin da Isra’ila key i wa al’ummar Palastinu kisan kiyashi, ba tare da ko daya daga cikin wadannan kasashe sun iya cewa uffan ba, sai dai wasu daga cikins kawa masu surutu a bayan fage.

3702472

 

http://iqna.ir/fa/news/3702472

 

 

captcha