IQNA

Amurka Ce Babbar Karfe Kafa Ga Duk Wani Yunkurin Samar Da Zaman Lafiya A Syria

22:50 - February 27, 2018
Lambar Labari: 3482436
Bangaren kasa da kasa, Mataimakin bababn sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya bayyana Amurka a matsayin babban karfen kafa ga duk wani yunkurin samar da sulhu da zaman lafiya a Syria.

Amurka Ce Babbar Karfe Kafa Ga Duk Wani Yunkurin Samar Da Zaman Lafiya A SyriaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, Tashar talabijin ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, Sheikh Na'im Kasim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yankin jabal na kasar Lebanon a yau.

Ya ce Amurka ummul haba'isin dukkanin rikicin da yake faruwa a Syria, bayan ta yi amfani da wasu kasashen larabawa da suke samar da 'yan ta'adda masu da'awar jihadi, tare da ba su makudan kudade da makamai domin rusa kasar Syria, a halin yanzu kuma Amurka ta shigo da kanta domin aiwatar da wannan aikin da kanta.

Sheikh na'im kasim ya ce babbar manufar hakan ita ce bayar da kariya ga Isra'ila, kasantuwar kasar Syria ita kadai ce kasa daya tilo daga cikin kasashen larabawan yankin da take taimaka ma Palstinawa wajen tunkarar zaluncin yahudawa da kuam kare wurare masu tsarki da ke Palastinu.

3694993

 

 

 

 

captcha