IQNA

‘Yan Ta’addan Boko Hara Sun Kashe Mutane 6 A Nigeria

22:29 - January 28, 2018
Lambar Labari: 3482343
Bangaren kasa da kasa, ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kasha mutane 6 a wani harin kunar bakin wake a kauyen Hyambula da ke cikin jahar Adamawa.

 

Kafanin dllancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na jaridar vanguardng ya habarta cewa, ‘yan ta’addan sun fara ne da yin harbeharbe bindga  acikin kayen, daga bisani kuma suka tayar da ba, inda suka kasha mutane shida.

Usman Abubakar shi ne kakakin rundunar ‘yan sanda a jahar Adamawa, ya bayyana cewa bayan wannan hari ‘yan ta’addan sun tafi da mutane da suka sace.

Ya kara da cewa a lokain da mayakan ‘yan ta’addan suka fara yin harbe-harbe, mutane sun yi ta gudu domin tsira da rayukansu, a lokacin ne wani dan kunar bakin wake daga cikin yan kungiyar fito daga bayan wata itaciya da ya boye, ya tarwatsa kasa.

Tuna  cikin shekara ta 2015 ce dai jahar Adamawa tak fuskantar matsalar ‘yan ta’adda na oko Haram masu dauke da akidar wahabiyanci, inda suke kashe mutane musulmi da wanda ba musulmi ba duk da sunan jihadi.

3685999

 

 

 

 

captcha