IQNA

Yan Boko Hara Sun kasha Musulmi Fiye da Dubu 5 A Najeriya

23:55 - January 01, 2018
Lambar Labari: 3482259
Bangaren kasa da kasa, Majalisar musulinci ta Najeriya reshen jahar Adamawa ta sanar da cewa sama da musulmi dubu 5 ne suka yi shahada sanadiyar hare-haren ta'addanci na kungiyar boko haram.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Cikin wani rahoto da ta kaddamar ga gwamnatin jahar, Majalisar musulinci ta Najeriya reshen Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da cewa daga shekaru 4 da suka gabata zuwa yanzu musulmi dubu biyar da 247 ne suka yi shahada yayin da wasu sama da dubu biyar da dari na daban suka jikkata sanadiyar hare-haren ta'addanci da kungiyar Boko haram ta kaddamar a jihar.

A yayin da Majalisar musulmi ke neman karin taimako ga iyalan wadanda rikicin kungiyar boko haram din ya ritsa da iyalansu tare kuma da sake gina wuraren ibada da makarantu, Majalisar ta bukaci karin daukan matakan tsaro da kuma karin taimakon kudi wajen taimakawa kungiyoyin dake taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da kungiyar boko haram.

Kididdiga da aka fitar ya nuna cewa, harin kungiyar boko haram din ya ritsa da wurare dubu 12 da 700 na al'umma da gwamnatin jihar ta Adamawa, daga cikin su gidaje, masallatai,da gonaki na fararen hula wanda idan aka kiyasta hasarar da harin ya janyo zai kai kimanin dalar Amurka miliyan dari biyu.

3678051

 

 

captcha