Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Harin dai an kai shi ne da asubahin yau Talata a wani masallaci dake garin na Mubu, kamar yadda kakakin 'yan sandan yankin, Osman Abubakar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaren Faransa na AFP.
Tun da farko dai alkalumman da hukumar agajin gaggawa a yankin ta fitar sun ce kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu a harin.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.