IQNA

An Mayar Da Martani Kan Masu Shishigi A Kan Yemen

23:54 - July 03, 2018
Lambar Labari: 3482804
Bangaren kasa da kasa, dakarun kasar Yemen sun samu nasarar mayar da martani kan mayakan ‘yanmamaya a yammacin kasar ta Yemen.

 

Rahotonin talabijin sun ce wani mai magana da yawun dakarun ya ce; Sojojin na Yemen sun kuma harbo wani sojan Saudiyyar guda da kuma da sansanin soja na al-Rumaih a gundumar jizan da ke kudancin Saudiyya.

A wani gefen, dakarun sa-kai na Ansarullah sun kashe 'yan koren Saudiyya masu yawa a yankin alriyah da ke kusa da babban birnin kasar Sanaa.

Kasar Saudiyya wacce take samun cikakken goyon bayan Amurka ta shelanta yaki akan kasar Yemen a watan Maris na dubu biyu da sha biyar wanda kawo ya zuwa yanzu an kashe fiye da mutane dubu sha biyu da jikkawa wasu dubbai.

3727309

 

captcha