IQNA

Amurka Na Shirin Aikewa Da Taimako Ga Saudiyya Ansarullah Sun Harba Makami A Kanta

23:42 - March 27, 2015
Lambar Labari: 3049250
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da Amurka ke shirin aikewa da wani Karin taimako zuwa ga mahkuntan Al Saud domin ci gaba da kashe al’ummar Yemen mayakan Ansarullah a nasu bangaren sun harba makami mai linzami a kan Saudiyya a matsayin martini.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Faransa cewa, batun aikewa da makamai ga Saudiya an gabatar da ita kuma ana tattauna ta.
A nasa bangaren jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya yi kakkausar suka a kan masarautar Al Saud da ke rike da madafun iko a Saudiyya, dangane da hare-haren da take jagoranta kan kasar Yemen.
Alhuti ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar, wanda gidajen talabijin na kasar Yemen suka watsa kai a daren jiya, inda ya bayyana cewa abin Saudiyya take yi abin kunya ne gare ta, domin kuwa ba a taba jin wani lokaci da ta jagoranci sojojin kasashen larabawa wajen kare al'ummar palastinu da Isra'ila ke kashewa tsawon shekaru fiye da sittin ba, amma kuma za ta iya nuna karfinta a kan al'ummar musulmi na kasar Yemen ta hanyar kasashe fararen hula a lokacin da suke barci a cikin dare tana yaki da kungiyar Huthi.
ya Ya ce yana kiran kasashen da Saudiyya ta saya da kudin man fetur domin suya  al'ummar Yemen da su canja shawara domin kare mutuncinsu a wurin al'ummominsu da kuma tarihinsu, ya ce a halin yanzu gwamnatin Saudiyya ba ta da wata kima a idon al'ummomin yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa kowa ya san cewa tana yi wa Amurka da yahudawa aiki, kuma idan su ba su san tarihin al'ummar Yemen ba, ita Saudiyya ta fi sanin mutanen Yenen, domin kuwa ta yi yaki da su a cikin shekarun da dubu da dari tara da talatin da biyu kuma ba ta ji da dadi ba, ya ce a yanzu ma tana son huce wancan haushin a kansu amma da wata hujjar ta daban, ya kara da cewa idan gwamnatin Saudiyya ta ci gaba da kai hari kan al'ummar Yemen, to za su dauki wasu matakai na daban wadanda ba su yi mata dadi ba, kuma zai jawo rikicin da ba a san ranar karewarsa ba tsakaninta da su.
3045212

Abubuwan Da Ya Shafa: ansarullah
captcha