IQNA

Jam’iyyar Al-wifagh A Bahrain Ta Yi Allawadai Da Harin ta’addancin Syria

17:01 - February 03, 2015
Lambar Labari: 2804014
Bangaren kasa da kasa, babbar jam’iyyar adawa ta alwifaq ta kasar Bahrain ta kakakusar da yin tir da Allawadai da harin ta’addancin da aka kai masu ziyarar Sayyidah Zainab (SA) a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya  naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwifagh cewa, a jiya jam’iyyar da ke kasar Bahrain ta kakakusar da yin tir da Allawadai da harin ta’addancin da aka kai masu ziyarar Sayyidah Zainab (SA) a kasar Syria wanda hakan yay i sanadiyyar zubar da jinin bayin Allah babu gaira babu sabar.
A cikin wani bayani da ta fitar jamiyyar ta Alwifag ta bayyana abin da ya faru da cewa hakika ya bayyana a fili cewa mutanen da suke aikata irin wannan ta’addanci, babbar manufarsu ita ce kawo ma muslunci cikas ko ta wane bangare, tare da tabbatar da cewa abin da suke yi ba zai taba tsorata masu bin tafarkin gaskiya na addinin muslunci da soyayya ga manzon Allah da iyalan gidansa ba.
Haka nan kuma wannan aiki bas hi da wata alaka da adinin muslunci da koyarwarsa, ko da kuwa masu yin hakan sun yi kokarin hada kansu da addinin muslunci ko kuma kiran abin abin da suke yi da cewaa  tafarkin addini ne.
Ya kara da cewa addinin muslunci na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai na duniya, ba tare da cin zarafin wani ko keta alfarmarsa ba.
2802859

Abubuwan Da Ya Shafa: hari
captcha