Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadi al-Balad cewa, Kholoud al-Mutairi ‘yar wasan katan Kuwait ta fice daga gasar ne bayan da aka zayyana sunanta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Thailand domin fuskantar wakiliyar gwamnatin sahyoniyawan.
Babbar sakatariyar kwamitin wasannin nakasassu ta Kuwait Sharifa al-Ghanim, a cikin wata sanarwa da jaridar Al-Ra'iyya ta kasar Kuwait ta fitar ta ce: Domin gwamnatin Sahayoniya ta kwace mana kasar Falasdinu, dole ne mu nuna rashin amincewa da halscinta.
Masu fafutuka na Kuwaiti sun yaba da matakin al-Mutairi. Abdallah al-Musawi wani mai bincike kan lamarin Palastinu ya bayyana cewa: Kuwait na ci gaba da zama a kan matsayinta a hukumance na kin amincewa da halascin Isra’ila. wanda kuma abin alfahari ne, domin daidaita alaka da Isra’ila cin amanar Palastinu ne.
A cikin 'yan watannin da suka gabata, wasu 'yan wasa daga bangarori daban-daban na kasar Kuwait, sun ki fuskantar abokan hamayya yahudawan sahyuniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.