IQNA

Taliban Ta Ce A Shirye Take Ta Kulla Alaka Da Amurka

23:58 - September 26, 2021
Lambar Labari: 3486355
Tehran (IQNA) Abdulsalam Hanafi mataimakin firayi ministan gwamnatin Taliban ya ce a shirye suke su kulla alaka da kasashen duniya da hakan ya hada har da kasar Amurka.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata  zantawa da ta yi da Abdulsalam Hanafi mataimakin firayi ministan gwamnatin Taliban, ya ce kungiyar a shirye take ta kulla alaka da kasashen duniya da hakan ya hada har da kasar Amurka.

Ya ce suna kara jaddada kira ga kasashen duniya da su amince da sabuwar gwamnatin Afghanistan, bisa la'akari da tasirin da kasar take da shi wajen yaki da ta'addanci, da kuma yaki da fataucin muggan kwayoyi.

Hanafi ya ci gaba da cewa, kulla alaka da gwamnatinsu yana da matukar alfanu ga kasashen duniya, kamar yadda hakan yake da alfanu ga kasar Afghanistan da al'ummarta.

baya ga haka kuma ya yi ishsra da cewa, kasantuwar China na daya daga cikin kasashe mambobi na din-din-din a kwamitin tsaron majalisar Dinkin Duniya, kuma tana da kyakkayawar alaka da sabuwar gwamnatin Afghanistan, akan haka China za ta iya taka rawa wajen kusanto da fahimtar kasashen duniya zuwa ga kulla irin wannan alaka da suke bukata.

kasashen duniya dai sun ki amincewa da gwamnatin Taliban a hukumance, amma wasu gwamnatoci sun nuna cewa a shirye suke su yi aiki da gwamnatin ta Taliban saboda kaucewa fadawar al'ummar Afghanistan cikin mawuyacin hali.

 

4000539

 

captcha