IQNA

Yahudawan Isra'ila Na Ci Gaba Da Keta lfarmar Masallacin Annabi Ibrahim (AS)

19:35 - September 23, 2021
Lambar Labari: 3486343
Tehran (IQNA) yahudawan Isra'ila na ci gaba da keta alfarmar masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke birnin Khalil

Kamfanin dilalncin labaran Falastinu ya bayar da rahoton cewa, a jiya daruruwan yahudawan sahyuniya ne tare da mara baya daga sojojin Isra'ila suka shiga cikin masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke birnin Khalil Falastinu tare da keta alfamar wannan masallaci.

Shugaban kwamitin masalalcin Sheikh Hifzi Abu Saninah ya bayyana cewa, yahudawan sun garkame masallacin Annabi Ibrahim ne tun daga lokacin faduwar rana a ranar Talta inda suka hana yin sallar magariba a cikin masalalcin, daga lokacin kuma har zuwa yau yahudawan suna cikin masallacin.

Yace yahudawan sun kutsa kai a cikin wannan masallaci ne tare da keta alfarmarsa, da sunan gudanar da bukukuwan idin yahudawa, wanda suke yi a kowace shekara a wannan lokaci, wada ake sa ran mai yiwa bayan kammala idin nasu su fice daga masallacin.

Tun a cikin shekara ta 1994 yahudawan suka fara yin wannan kutse a cikin masallacin Annabi Ibrahim da sunan gudanar da bukukuwan yahudawa na shekaras-shekara.

Birnin Khalil na gabar yamma da kogin Jordan ne, sannan kuma akwai matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna guda 400 a gefensa da gwamnatin Isr’ila ta gina, inda sojojin Isra’ila ke gadinsu dare da rana.

 
هتک حرمت حرم ابراهیمی از سوی شهرک نشینان صهیونیست + عکس
 
هتک حرمت حرم ابراهیمی از سوی شهرک نشینان صهیونیست + عکس
 
هتک حرمت حرم ابراهیمی از سوی شهرک نشینان صهیونیست + عکس
 
هتک حرمت حرم ابراهیمی از سوی شهرک نشینان صهیونیست + عکس

3999583

 

Abubuwan Da Ya Shafa: matsugunnan yahudawa
captcha