IQNA

Masu Ziyarar Arbaeen A Kan Hanyar Najaf Zuwa Karbala A Iraki

20:50 - September 22, 2021
Lambar Labari: 3486341
Tehran (IQNA) masu ziyarar arba'in suna kan hanyarsu zuwa birnin Karbala daga birnin Najaf

Tun fiye da mako guda da ya gabata ne masu ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) suka fara tattaki daga birane daban-daban na kasar Iraki zuwa birnin Karbala inda hubbarensa yake tare da zuriyar manzon Allah da aka kashe su tare da shi.

Wanann ziyara dai ana gudanar da ita fiye da shekaru dubu da dari uku da suka gabata, duk kuwa da cewa an yi sarakuna na dauloli daban-daban masu adawa zuriyar manzon Allah da suka rika hana wannan ziyara, amma dai har zuwa yau ana gudanar da ita.

Ana gudanar da wanann ziyara ne bisa dogaro da wasu ruwayoyi, mafi shahara daga ciki ita ruwayar Jabir Bin Abdullah Al-ansari (RA) wanda fitaccen sahabin manzon Allah (SAW) wanda ya yi wannan ziyara, kuma ya tabbatar da sahihancinta, wanda bayaninta ya zo a  cikin ruwayarsa mai tsawo.

 
 
 
 

3999355

 

captcha