IQNA

Ana Ci Gaba Da Mayar Da Martani Dangane Bai Wa Isra’ila Kujera A Tarayar Afirka

22:38 - July 30, 2021
Lambar Labari: 3486152
Tehran (IQNA) Ana ci gaba da mayar da martani dangane da baiwa gwamnatin yahudawan Isra’ila kujera a kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin mamba mai sanya ido.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sako da shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya aike wa babban kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka Musa Faki Muhammad, ya bayyana matukar damuwa kan wannan mataki da kungiyar ta dauka.

Haniyya ya bayyana cewa, wannan mataki ya saba wa abin da aka san siyasar kungiyar Tarayyar Afirka a kansa, na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falastinu da kuam fafutuka wajen kare hakkokinsu, domin kuwa bai wa Isra’ila wannan kujera a cikin kungiyar tarayyar Afirka, hakan yana a matsayin amincewa da dukkanin auukan da take aikatawa na kisan kiyashi akan al’ummar Falastinu.

A kan haka Haniyya, ya bukaci babban kwamishinan na kungiyar Tarayyar Afirka, da a sake yin nazari kan wannan mataki tare da janye shi, domin tabbatar da cewa tarayyar Afirka tana nan kan bakanta na kare wadanda ake zalunta, da kuma kin jinin duk wani nau’in mulki na zalunci da wariya  akan wasu al’umma.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Namibia ta fitar da wani bayani da  a cikinsa ta nisanta kanta daga matakin da kungiyar Tarayyar Afirka ta daukana baiwa Isra’ila kujera a cikin kungiyar, inda gwamnatin Namibia ta ce wannan ya hannun riga da tabbatattun ka’idoji na kungiyar, kuma tana yin Allawadai da hakan.

Kafin wannan lokacin ma kasashen Afirka ta kudu da Aljeriya sun fitar da bayanai da ke nuna rashin amincewarsu da wannan mataki, tare da bayyana cewa ba tare da amincewar dukkanin kasashen Afirka ne ba kungiyar ta yanke wannan shawara.

3987321

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin
captcha