IQNA

Rahoto: An Samu Karuwar Adadin Masallatai A Kasar Amurka

19:50 - June 03, 2021
Lambar Labari: 3485978
Tehran (IQNA) wani rahoto ya yi nuni da cewa, an samu karuwar adadin masallatai a kasar Amurka.

Jaridar Washington Post ta bayar da rahoton cewa, cibiyar musulmi ta (Islamic Society of North America) a Amurka ta bayar da rahoton cewa, duk da matakan da ake dauka na rufe masallatai, da kuma kin amincewa a gina masallataia  wasu yankyuna, amma duk da hakan adadin masallatai na musulmi a kasar Amurka yana karuwa.

Ihsan Bagby, ya harhada rahotanni a tsakanin shekara ta 2001 zuwa 2010 dangane da yanayin masallatai a kasar Amurka, inda bayyana cewa daga wancan lokacin zuwa yanzu an samu karuwar masallatai a kasar.

A cikin sabon rahotonsa wanda jaridar Washington Post ta buga ya bayyana cewa, a cikin shekara ta 2010 akwai masallatai 2106 a fadin kasar Amurka, amma zuwa karshen shekara ta 2020, adadin masallatan musulmi ya kai 2769.

Ya ce duk da ana takura musulmia  wasu yankunan na kasar Amurka wajen kin amincewa su gina masallatai, ko kuam rufe wasu masallatan da aka yi saboda wasu dalilai, amma duk da haka idan aka yi la’akari da adadin masallatai da aka fitar zuwa karshen 2020, za a lura da cewa adadin ya karu da kashi 31% a fadin kasar.

Haka nan kuma Bagby ya yi ishara da cewa, musulmi a kasar Amurka sun hada da al’ummomi daban-daban da suka fito daga bangarori daban-daban na duniya, daga yankin gabas ta tsakiya, da sauran kasashen larabawa da kasashen Asia gami da kasashen nahiyar Afirka.

Sai wani abu mai daukar hankali shi ne, Amurkawa bakaken fata ‘yan asalin Afirka su ne suka fi yawa daga cikin masu karbar addinin muslunci a kasar Amurka.

3975396

 

captcha