IQNA

A Senegal Musulmi Suna Daukar Nauyin Bizne Gawawwakin Mutanen Da Ba Sani Ba

20:00 - April 07, 2021
Lambar Labari: 3485790
Tehran (IQNA) musulmi suna bizne gawawwakin mutanen da ba a sani ba a kasar Senegal.

Kammfanin dillancin labaran Africa News ya bayar da rahoton cewa, shekaru 10 kenan musulmi suka kafa wani kwamiti wanda yake daukar nauyin bizne gawawwakin mutanen da ba a sani ba a kasar Senegal bisa koyarwa irin ta addinin muslunci.

Lamin Mandiang shi ne babban sakataren kwamitin na Association for Perfection and Mercy, wanda ke da mazauni a birnin Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal, ya bayyana cewa sun fara gudanar da wannan aiki tun a cikin shekara ta 2010.

Ya ce bias la’akari da cewa kasar Senegal kasa ce ta musulmi, saboda haka ya zama wajibi a yi la’akari da koyarwar addini wajen bizne gawawwakin da ba a sani ba, domin kuwa zato mafi rinjaye shi ne cewa su musulmi ne.

Ya ci gaba da cewa, ko ba komai addinin musulunci ya koyar da cewa a girmama gawar dan adam a suturta ta, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa aka kafa wannan kwamiti domin gudanar da wannan aiki.

Fiye da kshi 96 cikin dari na mutanen Senegal dai musulmi ne masu bin mazhabar Malikiyya.

 

3962927

 

captcha