IQNA

Ana Samun Karuwar Nuna Wa Musulmi Banbanci A Harkokin Kwallon Kafa A Burtaniya

23:53 - February 17, 2021
Lambar Labari: 3485663
Tehran (IQNA) sakamkon wani bincike da masana suka gudanar ya nuna yadda ake nuna wa musulmi banbanci a harkar kwallon kafa a Burtaniya.

Bisa ga binciken da masanan suka gudanar wanda ya hada da musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba a kasar Burtaniya, an iya gane cewa ‘yan wasa musulmi sun fi fuskantar matsaloli a cikin harkokinsu na wasa fiye da wadanda ba musulmi ba.

Sakamakon ya yi ishara da yadda yadda aka samu korafe-korafe da dama daga wasu daga cikin ‘yan wasa wadanda musulmi, dangane da yadda ake nuna musu banbanci ko kuma cin zarafinsu saboda addininsu.

Ana mika wadannan korafe-korafe a lokuta da dama ga hukumar kula da harkokin wasanni a kasar ta Burtaniya, amma ba tare da an dauki wani mataki wanda zai iya kawo karshen hakan ba.

‘Yan wasan suna bayyana cewa, sun fi fuskantar irin wannan matsala daga magoya bayan kungiyoyin da suke buga wa wasa, inda wasu lokuta akan sanya musu ihu, da furta kalmomi marassa kyau a kansu a lokutan wasa, musamman ma idan sun yi kure, wanda idan wani ya yi irin wannan kuren ba za a yi masa abin da ake yi a kansu ba.

Baya ga haka kuma mata musulmi da suke yin wasan kwallon kafa sanye da lullubi a kansu suna kokawa da irin matsalolin da suke fuskanta, wanda hakan yasa wasu da dama daga cikinsu a yanzu sun daina wasan kwallon kafa a kasar ta Burtaniya.

A cikin binciken da ka gudanar kan hakan, an gano cewa wasu mata musulmi sun fice daga kungiyar kwallon kafa ta jami’ar Birmingham City, sakamkon yadda ake cin zarafinsu saboda saka lullubi a kansu a lokacin wasa.

 

3954469

 

captcha