IQNA

Daesh Na Amfani Da Makarantun Kur’ani A Aljeriya Domin Yada Akidunta

20:06 - August 05, 2020
Lambar Labari: 3485058
Tehran (IQNA) kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh tana yin amfani da makarantun kur’ani a kasar Aljeriya yada akidunta.

Shafin yada labarai na Shurooq Online ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ‘yan ta’addan takfiriyya ta daesh tana yin amfani da makarantun kur’ani a kasar Aljeriya yada akidunta da kuma saka tsatsauran ra’ayi a cikin kwakwalen daliban kur’ani.

Kungiyar daesh ta fahimci cewa yin amfani da wannan hanyar yafi sauki wajen samar da irin mayakan da take bukata domin tura su aiwatar da ta’addanci a cikin kasar da ma wajenta, inda  ahalin yanzu ta wannan hanyar an tura daliban kur’ani da dama zuwa Mali domin su samo horo na yaki.

Jami’an tsaron kasar Aljeriya sun kame wasu daga cikin shugabannin irin wadannan cibiyoyi na kur’ani, wadanda kungiyar ta Daesh ke amfani da su wanke kwakwalen dalibai, tare da dora su bisa tafarkin ta’addanci da sunan jiahadi.

A cikin wanann makon an gurfanar da mutane biyar daga cikinsua  gaban kuliya, inda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru daga uku zuwa ashirin a  gidan kaso.

3914636

 

 

 

 

captcha