IQNA

Tilawar Kur’ani Da Minshawi Ya Yi Shekaru 57 Da Suka Gabata

19:58 - August 05, 2020
Lambar Labari: 3485056
Tehran (IQNA) an nuna wani faifan bidiyo na tilawar kur’ani mai tsarki da Muhammad Sadiq Munshawi ya yi a cikin dakin daukar hoto da sauti.

An dai haifi Munshawi ne a cikin shekara ta 1920 a garin Munsha da ke Masar, ya kuma hardace kur’ani tun yana da shekaru 8 a duniya.

Ya tashi a gidan makaranta kur’ani, mahaifinsa shi ne Sadiq Munshawi wanda ya kasance makarancin kur’ani, sai kuma kakansa shi ne Taif Munshawi, da kuma dan uwansa Mahmud sadiq Munshawi, wadanda dukkaninsu fitattun makaranta kur’ani ne.

Muhammad Sadiq Munshawi dai yana da salon karatu irin nasa, wanda ya shahara da shi a duniya, wanda kuma wanda ya yi irinsa to yana kwaikwayonsa ne.

3914789

 

 

captcha