IQNA

Yadda Ake Dinka Kyallen dakin ka’abah da Kuma Canja Shi

18:41 - July 30, 2020
Lambar Labari: 3485035
Tehran (IQNA) yadda ake gudanar da aikin dinkin kyallen dakin ka’abah da kuma yadda ake canja shi a kowace shekara.

A bisa al’ada a kowace shekara ana gudaar da aikin dinka sabon kyallen da ake lullube dakin Ka’abah da shi, inda a wannan shekara ma kamar sauran shekaru an canja wannan kyalle.

Duk da cewa dai a wananns heakara an gudanar aikin canja kyallen ne a lokacin da ake cikin mawuyacin hali na fuskantar cutar corona, inda adadi kalilan ne ke halartar aikin hajjin bana.

A cikin shekara ta 1438 sarkin saudiyya Salaman Bin Abdulaziz ya canja sunan cibiyar da ke dinka kyallen Ka’abah, zuwa cibiyar sarki Abdulaziz.

Wannan cibiya ita ce take da alhakin dinka kowane kyalle da za a yi amfani da shi domin lullube dakin Ka’abaha a kowace, kuma ana gudanar da canjin kyallen ne a daren Arafa, kamar yadda ya gudana a jiya.

A kan yi amfani da zaren alhariri mafi kyau a duniya wajen dinka wannan kyalle, tare da yin rubutu na ayoyin kur’ani da kuma kalmomi da suka kunshi sunayen Allah da manzo, domin kayata wanann kyalle kafin dora shi bisa ginin dakin Ka’abah mai alfarma.

A shekarar bana dai an takaita adadin masu aikin hajji ne saboda matsalar cutar corona da ta addabi duniya, domin kiyaye kamuwa da ita ko kuma yada ta.

3913480

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kyalle
captcha