IQNA

Musulmin Afrika Ta Kudu Sun Samu Izinin Ginin Wani Masallaci

23:08 - October 15, 2019
Lambar Labari: 3484156
Bangaren kasa da kasa, musulmin yankin Gordon Bay a kasar Afrika ta kudu sun samu izinin ginin masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayan kwashe tsawon shekaru 5 suna jira, , musulmin yankin Gordon Bay a kasar Afrika ta kudu sun samu izinin ginin masallaci.

Kasem Pir shugaban kwamitin muuslmin yankin Gordon Bay ya  bayyana cewa, tun daga shekara ta 2014 suke jiran hukuncin kotu a kan wannan batu.

Ya ce sun sayi wannan wuri da sunan gina wurin kasuwanci da kuma godajen zama, wanda fadinsa ya kai mita dubu biyu da 700, wanda kuma za a gina wa iyalai imanin 100 wurin salla da sauran ayyukan ibada a cikinsa.

Ya kara da cewa, duk da cewa a halin yanzu kotu ta bayar da iznin ginin masallaci a wurin, amma har yanzu akwai wadanda suke adawa da batun ginin masallacin, inda suka ce za su sake komawa kou domin neman a soke wannan lasisi da musulmi suka samu.

Dangane da sharadin kotu ta kafa musu kuwa ya bayyana cewa, an kafa musu sharadi kan cewa ba za su kiran salla yadda wanda ke wajen masallacin zai ji ba, kuma sun amince da hakan.

3850033

 

 

 

 

captcha