Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar kare hakkokin musulmi a Najeriya MURIC ta fitar a ta bakin shugabanta Ishaq Akintola, ta yi kakausar suka kan take hakkokin wasu dalibai musulmi a jami’ar Adeleke.
Bayanin ya ce daga cikin matakan da jami’ar take dauka na taka hakkokin musulmi har da tilasta su zuwa coci a ranar lahadi tare da sauran dalibai kiristoci.
Baya ga haka kuma tun kafin wannan lokacin an hana dalibai mata muuslmi saka hijabia cikin jami’ar, wanda a cewar kungiyar wannan ya sabawa tsarin doka na kasa da ‘yancin dan Najeriya.
Kungiyar ta kirayi hukumomin ilimi a kasar da su dauki matakan da suka dace domin takawa hukumomin wannan jami’a burki kan irin wadannan matakai da suke dauka.