IQNA

Masar Ta Yi Watsi Batun Binciken Mutuwar Morsi

22:50 - June 19, 2019
Lambar Labari: 3483752
Bangaren kasa da kasa, Masar ta yi kakkausar kan batun neman a gudanar da sahihin bincike kan mutuwar Muhammad Morsi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar Ahmad Hafez ya fadi yau cewa, ba su dadi furucun mai magana da yawun kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya kan batun mutuwar Muhammad Morsi.

Ya ce mutuwar Morsi mutuwa ce ta karar kwana, amma kuma ana neman mayar da batun ya zama na siyasa, wanda kuma a cewarsa gwamnatin Masar ba za ta taba amincewa da hakan ba.

Kakakin kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa akwai shakku dangane da mutuwar Morsi a lokacin da ake tsare da shi, a kan haka suna bukatar a gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru dangane da mutuwar tasa.

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a yau a garin Jiza  mahaifar Muhammad Morsi, domin yin Allawadai da gwamnatin kasar ta Masar, wadda suka zarga kai tsaye da hannu a cikin mutuwarsa.

3820661

 

 

captcha