IQNA

Muhammad Bin Salman Na Da Hannu A Kisan Khashoggi

22:45 - June 19, 2019
Lambar Labari: 3483751
Bangaren kasa da kasa, wani binciken majalisar dinkin duniya ya gano cewa yariman Saudiyya mai jiran gadon sarautar kasar yana da hannu dumu-dumu a kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran  Reuters ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai gudanar da ayyukan bincike na musamman Agnes Callamard, ta sanar da sakamkon binciken kwakwaf da ta gudanar kan kisan Jamal Khashoggi, inda daga karshe suka gane cewa Muhammad Bin Salman ne ke da alhakin kisan.

Callamard ta ce dukaknin bayanan da suka iya tattarawa dangane da kisan na Khashoggi, suna nuni da cewa yariman na Saudiyya shi ne ya dauki nauyin aikata wannan kisan kai, a kan haka dole ne  a dawo a gudanar da bincike na hakika kan wannan batu.

A ranar 2 ga watan Oktoban 2018 ne dai wasu jami’an tsaron Saudiyya da suka hada har da masu tsaron lafiyar Bin Salman su biyu, suka kashe Jamal Khasshoggi, bayan ya ziyarci ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na Turkiya.

Sakamakon binciken da jami’an Turkiya suka gudanar ya nuna cewa jami’an tsaron na Saudiyya sun yi amfani da zarto mai amfani da wuta wajen kashe tare da daddatsa gawarsa, kafin su sanya acid su narkar da gawar.

Da farko dai Saudiyya ta musunta bacewar Khashoggi a cikin ofishin nata, amma bayan tabbatar da dalilai kan hakan ta amince da kisan, amma ta dora alhakin hakan a kan wadanda suka aikata kisan kawai, ba tare da bayyana wanda ya sanya su aikata hakan ba.

3820826

 

 

captcha