Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Al-ra’ay ta kasar Jordan ta bayar da rahoton cewa, a yau Asabar an bude gasar kur’ani ta duniya a birnin Aman na kasar Jordar tare da halartar wakilai daga kasashe 38 na duniya.
Rahoton ya ce gasar za ta tabo dukkanin bangarori da aka saba gudanar da ita, kuma daga karshe za a bayar da kyautuka ga mutane 5 da suka fi nuna kwazo a gasar.
A gasar shekarar da ta gabata Muhamamd rasul takbiri daga kasar shi ne ya wakilci kasar a wannan gasa, inda ya kasance daga cikin wadanda suka yi gasar a bangaren karatu.
Wannan dais hi ne karo na ashirin da shida ake gudanar da irin wannan gasa ta kasa da kasa a Jordan, tare da halartar kasashen duniya.