IQNA

Larijani: Al’ummomin duniya Sun Bayyana Matsayinsu Kan Yarjejeniyar Karni

23:57 - June 09, 2019
Lambar Labari: 3483722
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa, al’ummomin duniya sun bayar da kyakkyawar amsa ga masu hankoron sayar da Falastinu da sunan yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A lokacin da yake gabatar da jawabi a yau gaban majalisar dokokin kasar Iran bayan dawowa hutun salla, Larijani ya bayyana cewa, jerin gwanon ranar Quds da aka gudanar a Iran da sauran kasashen duniya, na musulmi da ma wadanda ba na musulmi babbar amsa ga yarjejeniyar karni.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin al’ummar Falastinu bakinsu ya zo daya wajen kin amincewa da abin da ake kira yarjejeniyar karni, kamar yadda al’ummomin muslmi da ma masu ‘yancin siyasa a duniya ba su amince da ita ba, in banda wadanda suka kirkiro ta da  kuma wasu daga cikin wadanda suka sayar da kansu ga ‘yan mulkin mallaka.

Dangane da matsin lambar Amurka a kan kasar Iran kuwa, Larijani ya jaddada cewa, babu abin da hakan zai kara wa Iran sai jajircewa da ci gaba da kara daukar matakai na dogara da kanta.

 

3817799

 

 

captcha