IQNA

An Bude Bangaren Kasa Da Kasa A Baje Kolin Littafai

23:56 - May 13, 2019
Lambar Labari: 3483636
Bangaren kasa da kasa, an bude bangaren kasa da kasa a baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, an bude bangaren kasa da kasa  a wannan bababn baje kolin kur'ani na kasa da kasa da ke samun halartar bangarori daban-daban daga cikin gida da kuma kasashen duniya.

Mamhud Wa'izi wanda shi ne babban jami'i mai kula da bangaren kasa da kasa, a wannan baje koli ya bayyana cewa, daga abubuwan da aka baje a wanann bangaren akwai littafai na Urdu, Ingilishi, Larabci, da Turkanci, da kuma mujallar Tunisia.

Pakistan ita ce babbar bakuwar bangaren, haka nan kuma kasashen ad suke halarta sun hada da Iraki, malaysia, Yemen, Afghanistan Tunisia da sauransu.

3811165

 

captcha