IQNA

Liberation: Turkiya Na Hankoron Kutsawa A Nahiyar Afrika

22:11 - February 20, 2019
Lambar Labari: 3483389
Bnagaren kasa da kasa, jaridar Liberation ta kasar Faransa ta bayar da rahoton da ke cewa Turkiya na hankoron yin kutse a cikin Afrika.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Liberation ta kasar Faransa ta bayar da rahoton da ke cewa Turkiya na hankoron yin kutse a cikin Afrika ta hanyar gudanar da wasu ayyuka na jan hankalin al’ummomin yankin, na baya-bayan nan shi ne ginin masallaci a Jibouti.

Jaridar ta ce Turkiya ta gina masallaci mafi girma  akasar Jibouti tare da bayar da shi a matsayin kyauta ga gwamnatin kasar.

Haka nan kuma jaridar ta kara da cewa a cikin shekaru 15 da Erdogan ya karbi mulkin Turkiya ya yi tafiya sau 40 zuwa kasash3 26 na nahiyar Afrika.

Kamar yadda kuma a cewar jarida ya gina masallatai da makarantu a cikin kasar Sudan, da kuma wasu cibiyoyi na addini da na jin kai, da nufin yin tasiri kan tattalin arzikin kasar da ma siyasarta.

3791763

 

 

 

 

 

captcha