Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia today ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin tsaro a kasar Masar sun sanar da cewa a jiya an zartar da hukuncin kisa a kan wasu mambobi a kungiyar Ikhwan Muslimin a Masar su uku, bisa laifin kisan Nabil Faraj, wani babban jami’in ‘yan sanda na kasar Masar.
Tun shekaru 5 da suka gabata ne dai aka kasha Nabil Faraj a yankin Kardasa bayan kai wani hari.
Jami’an tsaron Masar 13 ne aka kasha a harina cikin watan Agustan 2013, inda wasu mutane dauke da manyan bindigogi suka kaddamar da hare-hare a kan cibiyoyin tsaro, inda ake tuhumar wadannan mutane 3 da cewa suna daga cikin wadanda suka kaddamar da harin, kuma an zartar da hukuncin kisa akansu.