IQNA

Gwamnatin China Na Ci Gaba Da Take Hakkokin Musulmi

23:21 - February 13, 2019
Lambar Labari: 3483369
Bangaren kasa da kasa, Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun fitar da rahotanni kan irin cin zalun da gwamnatin kasar China take yi kan musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun saka wani faifan bidiyo a cikin shafin youtube, wanda ke nuna cin zalun da gwamnatin kasar China take yi kan musulmin kasar tare da kuntata musu.

A cikin shekarun baya-bayan nan dai gwamnatin kasar China tana daukar matakai wadanda suka yi hannun riga da dukkanin ka’idoji da dokoki na duniya wajen takura muuslmin kasar, wadanda su ne marassa rinjaye.

Rahoton ya ce a cikin ‘yan lokutan da suka gabata, gwamnatin kasar ta China ta gina wasu sansanoni guda dubu da 200 da nufin tsugunnar da musulmi a cikinsu wadanda aka kora daga yankunansu, wanda kuma sansanonin za su iya daukar mutane miliyan daya zuwa miliyan biyu.

Annan mataki ya sanya kungiyoyin kare hakkin bil adama a ko’ina cikin fadin duniya suna yin Allawadai da wanann mataki da gwamnatin kasar ta China take dauka a kan musulmin kasar, wadanda suke da hakkoki kamar sauran dukkanin ‘yan kasar ba tare da wani banbanci ba.

3789613

 

 

captcha