IQNA

Babban Sakataren UN Ya Mayar Da Martani Kan Kisan Khashoggi

23:59 - October 20, 2018
Lambar Labari: 3483060
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya mayar da martani dangane da kisan gillar da Saudiyya ta yi wa Khashoggi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sputnik cewa, Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guturres ya mayar da martani dangane da kisan gillar da Saudiyya ta yi wad an jarida kuma marubuci Jamal Khashoggi.

Guterres ya bayyana cewa hakika ya kadu matuka da jin labarin kisan Khashoggi, kuma ya zama wajibi a gudanar da bincike na kasa da kan wannan batu.

Da farko Saudiyya ta musunta cewa Khashoggi ya bata a cikin ofishinta da ke Istanbul a Turkiya, amma bayan shudewar kwana goma sha takwasa sakamakon matsin lamabar duniya, a yau ta fito ta amsa cewa cewa a cikin ofishin nata aka kasha shi, amma ta hanyar fada tsakaninsa da masu bincike.

Wannan bayani da Saudiyya ta fitar dai bai gamsar da mafi yawan kasashen duniya ba, inda suke ci gaba da neman Saudiyya da ta yi bayani kan yadda aka kasha Khashoggi a  cikin ofishinta.

3757151

 

 

 

 

captcha