IQNA

An Kawo Karshen Bayar Da Horo Kan hardar Kur'ani A Mauritania

23:49 - August 16, 2018
Lambar Labari: 3482897
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen wani wani shirin bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a a birnin Nuwakshout na Mauritaniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-akhbar cewa, an gudanar da wannan shiri ne a cikin kankanin lokaci.

Dukkanin wadannan suka cikin shirin dalibai 59 ne da suka hada da yara maza da mata, inda tsarin hardar ya fara daga juzui 10 abin ya yi sama.

An fara gudanar da wannans hiri ne tun daga lokacin da aka bayar da hotun baraza, domin yara su yi amfani da wannan damar wajen hardar kur'ani mai tsarki.

Wuld Sayyid Hajj shugaban cibiyar hadar kur'ani ta kasar Mauritaniya ya yaba da yadda shirin ya gudana, ya kuma bayyana cewa da yardarm Allah za a ci gaba da gudanar da shi a shekaru masu zuwa.

3738991

 

captcha